Rundunar haɗin gwiwa ta Operation HADIN KAI ta kama mutane biyar kan zargin şu da yin harbin da ya kashe wata yarinya a Maiduguri, babban birnin jihar Borno. ba bisa ka’ida ba a jihar Borno.
Lamarin ya faru ne a yankin Ngomari da misalin ƙarfe biyu na rana a ranar 4 ga Afrilu, 2026, lokacin da wasu ‘yan banga masu alaƙa da tawagar tsaron shugaban wata ƙaramar hukuma suka rika harbi sama yayin bikin aure a rukunin gidajen malaman makarantar Umaru Musa Yar’Adua.
Rundunar ta ce an kama waɗanda ake zargi kuma za a miƙa su ga hukumomin da suka dace domin bincike da gurfanar da su, tana mai jaddada cewa ba za a lamunci amfani da makamai ba bisa ka’ida ba.