Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Sojojin Najeriya sun kashe ‘kasurgumin’ dan bindiga a Zamfara

Rahotanni sun bayyana cewa rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar kashe wani kasurgumin dan binidiga da ya shahara a kafafen sada zumunta, musamman TikTok, mai suna Alti, wanda ya addabi yankunan da ke kan hanyar Gusau zuwa Funtua da sauran yankunan Arewa maso Yammacin Najeriya.

Wata majiya daga hedikwatar sojojin ta shaida wa kamfanin dillancin labarai ta Najeriya (NAN) cewa an kashe Alti ne a wani samame da sojoji suka kai maboyarsa a kwanakin nan.

Ana kallon lamarin a matsayin babbar illa ga ƙungiyoyin ‘yanbindiga a jihohin Zamfara da Katsina da kuma wasu sassan jihar Sokoto.

Duk da ƙarancin shekarunsa, Alti ya zama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin ‘yan bindiga a yankin, inda ake zargin yana gudanar da sansanoni daga kudancin Gusau har zuwa yankunan Jibiya da Funtua.

Daga waɗannan wurare, yaransa ke kai hare-hare tare da sace mutane domin neman kuɗin fansa, sannan su kan kai farmaki a hanyoyi, har ma da amfani da bama-bamai a manyan tituna.

An kuma bayyana cewa Alti ya shahara a tsakanin ‘yan bindiga da lakabin “bankin kuɗi” saboda yadda yake sarrafa kuɗaɗen fansa daga sace-sacen mutane, tare da bayyana a bidiyoyin TikTok yana nuna makamai da yin barazana.

Masana harkokin tsaro sun ce kashe Alti na iya rage ayyukan sace-sacen mutane a yankin Zamfara zuwa Katsina, tare da raunana ƙungiyoyin ‘yan bindiga da ke biyayya gare shi.

Mazauna yankin dai sun dade suna fama da hare-hare da garkuwa da mutane, inda galibi ake biyan kuɗaɗen fansa masu yawa, abin da ya sa kashe manyan shugabannin ‘yan bindiga kamar Alti ke da muhimmanci wajen dawo da zaman lafiya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use