Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Spain ta bukaci Isra’ila ta dakatar da kai hari Lebanon

Spain ta bukaci Isra’ila ta dakatar da kai hari Lebanon Spain ta bukaci Isra’ila ta dakatar da kai hari Lebanon
Ministan harkokin wajen Spain, Jose Manuel Albares, ya ce dole ne Isra’ila ta dakatar da kai hare-hare kan Lebanon.

Ministan harkokin wajen Spain, Jose Manuel Albares, ya ce dole ne Isra’ila ta dakatar da kai hare-hare kan Lebanon.

“Mun yi kira a yi sassauci, amfani da diflomasiyya da komawa kan tattaunawa,” in ji shi, sannan ya kara da cewa, “ya kamata a dakatar da yaki, kuma a tabbatar cewa Iran da kungiyoyin da ke tare da ita sun daina kai hare-hare a kasashen yankin,” kamar yadda ya fada a hira da Aljazeera.

Albares ya ce dole Lebanon ta kasance cikin tsarin zaman lafiya da yarjejeniyoyin da ake tattaunawa a kansu.

Ya kara da cewa Spain na goyon bayan hukumar wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Lebanon UNIFIL, kuma tilas ne a dakatar da kai hari.

An kirkiri UNIFIL a watan Maris 1978 don tabbatar da ficewar Isra’ila daga Lebanon, mayar da zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa, da kuma taimakawa gwamnatin Lebanon wajen dawo da iko a yankin.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use