Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Tunji Disu, ya bukaci babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta yi watsi da karar neman hakki da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
El-Rufai ya shigar da karar ce bayan jami’an Hukumar ICPC tare da ‘yan sanda sun kai samame gidansa da ke Abuja domin bincike.
Ya buƙaci kotun ta ayyana samamen da aka kai gidansa a matsayin wanda aka yi ba bisa ka’ida ba, ta hana hukumomi amfani da duk wani abu da aka ɗauka daga gidansa a matsayin shaida, sannan a biya shi Naira biliyan 1 a matsayin diyya saboda abin da ya kira tauye masa hakki.
Sai dai, IGP ya roki kotun ta yi watsi da karar gaba ɗaya inda ya bayyana cewa binciken da aka yi a gidan El-Rufai ya samu takardar izinin kotu kuma jami’an tsaro sun bi duk matakan doka wajen gudanar da aikin.
Haka kuma ya zargi tsohon gwamnan da kokarin amfani da kotu domin kauce wa bincike da kuma tuhumar da hukumomi ke yi masa.
Ana sa ran kotun za ta ci gaba da sauraron karar a ranar 25 ga Maris domin yanke hukunci kan bukatun bangarorin biyu.