Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya umarci masu mukamai da aka nada a gwamnatinsa da ke sha’awar tsayawa takara a zaben 2027, cewa su ajiye aiki nan da makonni biyu.
Sanarwar da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin ta bayyana cewa masu son tsayawa takarar za su fara murabus daga yau har zuwa ranar 31 ga watan Maris.
Shugaba Tinubu yace, wannan mataki ya zama dole, saboda a tabbatar an bi duk wata ka’ida da hukumar zabe ta fitar, don samun sahihin sakamako a zabukan 2027 dake tafe.