Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Tinubu ya bayar da umarnin jibge dakarun tsaro a Kwara 

Tinubu ya yi Allah-Wadai da kashe-Kashe a Filato da Kaduna Tinubu ya yi Allah-Wadai da kashe-Kashe a Filato da Kaduna
Tinubu ya yi Allah-Wadai da kashe-Kashe a Filato da Kaduna

Bayan wani mummunan hari da ‘yan ta’adda suka kai a jihar Kwara da ke arewa maso tsakiyar Najeriya a ranar Laraba Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin tura jami’an tsaro don samar da zaman lafiya a yankin.

Harin ya yi ajalin rayukan mutum 160 tare da kona dukiya da shagunan jama’a.

Fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwa ta bakin mai bai wa shugaban shawara kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga inda ya ce Tinubu ya bayar da umarnin aikewa da bataliyar sojojin ne don kare rayukan sauran alummar yakin da abin ya shafa.

 Kazalika, shugaba Tinubu ya nuna bacin ransa kan afkuwar lamarin, yana mai cewa wadannan yan ta’adda sun nuna hali na rashin Imani wajen aikata kisan da suka yi.

Har ila yau, sanarwar ta kara da cewa jami’an tsaron da aka tura za su sanya idao kan duk wani abu da ke da jibi da tsaron rayuka da dukiya na wannan yakin, tare da kira ga gwamnatin jihar ta ba da hadin kai ga jami’an tsaron da aka aika don tabbatar da zaman löafiya.

zuwa yanzu adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya kai mutum 160 ciki harda sarakunan gargajiya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use