Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Tinubu ya musanta zargin tilasta wa ‘yan siyasa sauya sheka zuwa APC

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya ya musanta zargin cewa gwamnatin sa na tilasta wa ‘yan siyasa ko hana ‘yan adawa magana, yana mai cewa babu wanda aka tilasta wa ya koma jam’iyyar APC ko aka yi amfani da karfin gwamnati a kansa.

Tinubu ya bayyana hakan ne a wani taron buda-baki da ya yi tare da sanatoci a fadar shugaban kasa da ke Abuja yana mai cewa yanke shawarar sauya sheka da wasu ‘yan siyasa ke yi yana fitowa ne daga ra’ayin kansu, ba tilastawa ba.

Shugaban ya jaddada cewa matsalolin tsaro kamar ta’addanci da ‘yan daba na ƙara dagula siyasa, yana mai kira ga shugabanni su mai da hankali kan hadin kai da karfafa dimokuradiyya, tare da sanya muradin ƙasa a gaba fiye da kishin jam’iyya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use