Shugaban Nageriya Bola Ahmed Tinubu ya roki Majalisar Dattawa da ta sauya kundin tsarin mulki domin ba da damar kafa ‘yan sandan jihohi.
Ya bayyana bukatar a wani taron buda-baki da ya yi tare da sanatoci a fadar shugaban ƙasa a ranar Laraba.
Tinubu ya ce ‘yan sanda na jiha suna da muhimmanci wajen magance matsalolin tsaro, inganta aikin ‘yan sanda a matakin ƙasa, da ba jihohi damar mayar da martani cikin sauri ga barazanar tsaro.