Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Tinubu ya sha alwashin murƙushe barazanar tsaro a Najeriya

Tinubu Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sha alwashin kara kaimi wajen shawo kan matsalar tsaro a fadin kasar.

Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Lahadi lokacin da ya karbi bakuncin mataimakinsa Kashim Shettima da wasu gwamnoni 23 na kasar wadanda suka kai masa gaisuwar sallah a gidansa da ke Legas.

Tinubu ya ce ya tattaunauwar da ya yi lokacin ziyarar aiki da ya kai Birtaniya ta mayar da hankali ne kan tsaro da jin daɗin al’umma, tare da nemo hanyoyin samun kayan aiki da tallafi daga ƙasashen waje.”

Ya ƙara da cewa ya tattauna da shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron kan haɗin gwiwa wajen samar da kayan tsaro da tallafi.

Ggwamnati na ƙoƙarin ƙarfafa alaƙa da sauran ƙasashe domin inganta tsaro, rashin tsaro babbar barazana ce ga ci gaba da walwalar ƙasa,” in ji shugaban.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use