Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Tinubu ya yi Allah-Wadai da kashe-Kashe a Filato da Kaduna

Tinubu ya yi Allah-Wadai da kashe-Kashe a Filato da Kaduna Tinubu ya yi Allah-Wadai da kashe-Kashe a Filato da Kaduna
Tinubu ya yi Allah-Wadai da kashe-Kashe a Filato da Kaduna

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kakkausar suka kan hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane a jihohin Filato da Kaduna, inda ya bayyana su a matsayin muggan laifuka marasa imani da tausayi.

Rahotanni sun nuna cewa hare-haren sun faru ne a yankin Jos (Angwan Rukuba) da kuma wani ƙauye a Kaduna, inda aka kashe mutane tare da sace wasu, ciki har da baƙin aure.

Tinubu ya tabbatar wa al’ummar Najeriya cewa duk masu hannu a cikin wannan ta’asa za su fuskanci hukunci, tare da umartar jami’an tsaro su ƙara ƙaimi wajen farautar waɗanda suka aikata laifin.

Shugaban ya kuma yi gargaɗi kan yaɗa ƙarya ko bayanan da za su iya tayar da rikici, yana mai jaddada cewa dole ne a haɗa kai domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Haka kuma, ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, tare da yaba wa gwamnonin jihohin biyu kan matakan da suke ɗauka wajen shawo kan matsalar tsaro.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use