Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da kafa wani asusu na musamman domin tallafa wa sojojin Najeriya, ciki har da wadanda suka jikkata da iyalan wadanda suka mutu a bakin aiki, yayin da yake bikin cika shekaru 74 da haihuwa.
Shugaban ƙasar ya bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi cewa ya umurci Babban Akanta na Tarayya da ya bude asusu na musamman domin wannan shiri.
Ya kuma yi alƙawarin bayar da dukkan albashinsa tun daga lokacin da ya hau kujerar shugaban ƙasa a matsayin kuɗin farko don tallafa wa wannan asusu.
“Ina roƙon Gwamnoninmu, ‘yan Majalisar Tarayya, kamfanoni masu zaman kansu, abokaina da duk masu goyon baya da su tallafa wa wannan shiri. Cikakkun bayanai kan asusun za su fito nan gaba kadan,” in ji shi.