Yayin da hadarin giza-gizon zaben shekarar 2027 ke hadowa, ana sa ran zuwan shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu garin Kano a ranar Litinin don tarbar gwamnan kano Abba Kabir Yusuf zuwa jam’iyyar APC a filin wasa na Sani Abacha dake Jihar.
Kazalika ana sa rai da zuwan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da sauran gwamnonin jam’iyyar ta APC
Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas ya ce, taron zai bai wa gwamnan damar zama cikakken dan jam’iyyar, inda ya ce wannan ci gaba ne ga APC da ma siyasar jihar da kasa baki daya.
Tuni dai aka fara nada shugabannin da za su jagoranci kwamitocin da za su kula da taron har a kammala.
Daga cikin wadanda za su jagoranci kwamitocin akwai dan gidan tsohon gwamnan Kano Umar Abdullahi Ganduje da tsohon kwamishinan yada labarai a zamanin Gandujen, Muhammad Garba da kuma Kanal Umar Malami wanda shi ne zai jagoranci kwamitin kula da ayyuka na musamman.