Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Tinubu zai samu nasara da gagarumin rinjayi a Arewa – Shehu Sani

Tinubu zai samu nasara da gagarumin rinjayi a Arewa - Shehu Sani Tinubu zai samu nasara da gagarumin rinjayi a Arewa - Shehu Sani
Tinubu zai samu nasara da gagarumin rinjayi a Arewa - Shehu Sani

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Shugaban Najeria, Bola Tinubu, zai samu nasara mai yawa a yankin Arewacin Najeriya a zaɓe mai zuwa.

Sani ya bayyana hakan ne yayin wata hira, inda ya ce ana ci gaba da shirye-shirye musamman a jihar Kaduna domin tabbatar da cewa shugaban ƙasar ya samu kuri’u masu yawa a yankin.

Ya ƙara da cewa, duk da ƙalubalen da aka fuskanta a zaɓen da ya gabata, yanzu al’amura sun daidaita, yana mai nuna cewa shugabancin da Tinubu ya taimaka wajen haɗa kan al’umma tsakanin Arewa da Kudu.

A cewarsa, wannan haɗin kai zai ba Bola Ahmed Tinubu damar samun rinjaye mai yawa a Arewacin Najeriya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use