Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa Amurka na duba yiwuwar kawo karshen hare-haren soja da take kai wa ƙasar Iran, inda ya ce ƙasashen duniya da ke amfani da Mashigar Hormuz su su sanya ido tare da kula da ita.
A cikin wani saƙon da ya wallafa a shafin sada zumunta na Truth, Trump ya ce “mun kusa cim ma muradunmu, don haka muna duba yiwuwar kawo ƙarshen ayyukan sojojinmu a Gabas ta Tsakiya kan gwamnatin ta’addanci ta Iran.”
Ya ƙara da cewa ya kamata ƙasashen da ke amfani da Mashigar Hormuz su kula da ita da sanya ido a kanta, yanamai cewa “Amurka ba za ta yi hakan ba.”