Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Trump ya ce Amurka ta lalata jiragen ruwan Iran 42

Shugaban Amurka, Donald Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce sojojin ƙasar sun cimma nasarori masu yawa a yaƙin da ake yi da Iran, da haɗin gwiwar Isra’ila.

Da yake jawabi yayin wani taro na shugabannin ƙasashen Latin Amurka a Florida, Trump ya ce cikin kwanaki uku na fafatawa, Amurka ta lalata jiragen ruwan rundunar sojin ruwa ta Iran guda 42, inda ya ce wannan ya girgiza ƙarfin rundunar sosai har suka daina aiki.

Trump ya kuma yi ikirarin cewa an “ƙwace” ƙarfin rundunar sama ta Iran da tsarin sadarwarsu, wanda yanzu ba sa iya gudanar da ayyukansu na yau da kullum yadda ya kamata.

Trump ya bayyana cewa wannan mataki na soja ba kawai ya shafi rundunar Iran ba ne, har ma da tasirin tattalin arziki da sufuri a yankin Gabas ta Tsakiya, musamman a wuraren jigilar mai kamar Strait of Hormuz, inda suke jigilar mai mai yawa daga yankin.

Haka kuma, Trump ya ce zai kai ziyarar ta’aziya wa iyalan sojojin Amurka da suka mutu a yaƙin, inda ya kira su “manyan jaruman ƙasarmu”.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use