Tsohon ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kebbi a zaɓen 2023, Janar Aminu Bande, ya sanar da ficewa daga jam’iyyar.
A cikin wasiƙar murabus ɗin da ya aikawa shugaban jam’iyyar na mazabarsa a Birnin Kebbi, Bande ya ce ya yanke shawarar ne bayan tattaunawa da nazari mai zurfi tare da magoya bayansa da masu ruwa da tsaki.
Ya bayyana cewa ficewar tasa na da nufin neman wata sabuwar hanya da za ta ba shi damar ci gaba da fafutukar samar da ingantaccen shugabanci a Kebbi da Najeriya baki ɗaya.
Sai dai har yanzu bai bayyana sabuwar jam’iyyar da zai koma ba, duk da cewa ana hasashen cewa sauyin nasa na da alaƙa da shirye-shiryen siyasar shekarar 2027.