Hukumar ƙwallon kafa ta Turai, Uefa, ta dakatar da ɗan wasan Benfica, Gianluca Prestianni buga wasa ɗaya bayan zarginsa da yi wa Vinicius Jr kalaman wariya yayin fafatawarsu a gasar Champions League a makon jiya a Portugal.
UEFA ta sanar da wannan dakatarwa ta wucin gadi a ranar Litinin, bayan naɗa kwamitin da zai gudanar da bincike kan lamarin.
Vinicius ya shaida wa alkalin wasa Francois Letexier cewa ɗan wasan tawagar Argentina ya yi masa kalaman wariya a wasan cike gurbin shiga zagaye na biyu a Champions League da Real Madrid ta ci 1-0 ranar Laraba.
Hukumar ta ce za a iya ɗaukar ƙarin matakan ladabtarwa da zarar ta kammala binciken.
Real Madrid da Benfica za sake haɗuwa a wasa na biyu a birnin Madrid ranar Laraba.