Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

UEFA ta dakatar da Prestianni na Benfica buga wasa ɗaya

Madrid vs Benfica Madrid vs Benfica
Madrid da Benfica za su ƙara haduwa ranar Laraba (Getty Images)

Hukumar ƙwallon kafa ta Turai, Uefa, ta dakatar da ɗan wasan Benfica, Gianluca Prestianni buga wasa ɗaya bayan zarginsa da yi wa Vinicius Jr kalaman wariya yayin fafatawarsu a gasar Champions League a makon jiya a Portugal.

UEFA ta sanar da wannan dakatarwa ta wucin gadi a ranar Litinin, bayan naɗa kwamitin da zai gudanar da bincike kan lamarin.

Vinicius ya shaida wa alkalin wasa Francois Letexier cewa ɗan wasan tawagar Argentina ya yi masa kalaman wariya a wasan cike gurbin shiga zagaye na biyu a Champions League da Real Madrid ta ci 1-0 ranar Laraba.

Hukumar ta ce za a iya ɗaukar ƙarin matakan ladabtarwa da zarar ta kammala binciken.

Real Madrid da Benfica za sake haɗuwa a wasa na biyu a birnin Madrid ranar Laraba.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use