Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Wata kungiya ta zargi ’yan Kwankwasiyya da rura wutar siyasa a Kano

Kwankwaso Kwankwaso
Kwankwaso ya ce ya zama tilas a sama wa ‘yan Najeriya mafita (Kwankwaso/X)

Wata kungiya a Kano ta zargi jagoran Kwankwasiyya Rabiu Musa Kwankwaso da ingiza matasa mabiyansa domin rura wutar rikicin siyasa a Kano.

Shugaban kungiyar a jihar, Datti Tukur, ya ce wasu matasa masu alaƙa da tafiyar na amfani da kafafen sada zumunta wajen sukar manyan ‘yan siyasa, ciki har da Abba Kabir Yusuf da Abdullahi Umar Ganduje, tare da wasu da ake ganin ba sa goyon bayan akidar Kwankwaso.

Ƙungiyar ta kuma yi zargin cewa wasu daga cikin mabiyan sun wallafa hotuna izgilanci ga Gwamna Yusuf, lamarin da ta ce na iya ƙara dagula yanayin siyasa a jihar.

Sai dai har zuwa yanzu, babu wata sanarwa kai tsaye daga ɓangaren Kwankwasiyya kan waɗannan zarge-zarge.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use