Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Wike ya bukaci ‘yan PDP su hada kai don ciyar da jam’iyyar gaba

Jam'iyyar PDP Jam'iyyar PDP
Wike ya ce PDP ta fara farfaɗowa daga matsalolin da ta shiga (PDP)

Ministan babban birnin tarayya Abuja kuma jigo a jam’iyyar PDP, Nyesom Wike ya bukaci dukkanin ‘ya’yan jam’iyyar da su ajiye duk wani bambancin ra’ayi su hada kai don ciyar da jam’iyyar gaba.

Hakan na zuwa ne bayan soke shugabancin tsagin Tanimu Turaki a PDP da kotun daukaka kara tayi a ranar Litinin.

Wike ya ce babu wata jam’iyyar hamayya a Najeriya fa ce PDP, sannan jam’iyyar APC ce mai mulki, don haka idan ba ka cikin wadannan jam’iyyun biyu, ko shakka babu ba ka da jam’iyya.

Kazalika ya kara da cewa duk wadanda suka je suka yi taro da sunan jam’iyyar a wata jiha, su san cewa hakan babban kuskure ne kuma karya dokar kundin mulkin kasa ne da ta hukumar zabe.

Tuni ministan ya ayyana wadanda za su ci gaba da jagoranci har zuwa lokacin da al’amura za su daidaita a cikin jam’iyyar.

Wike ya kuma jagoranci kafa kwamiti na musamman da zai sanya ido kan taron jam’iyyar da za a kara yi ranar 29 da kuma 30 ga watan Maris din da muke ciki.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use