Wani masanin harkokin tsaro a Najeriya, Dakta Kabiru Adamu, ya bayyana cewa akwai damuwa game da shigowar dakarun Amurka zuwa Najeriya ba tare da an bayyana wa ‘yan kasa ainihin yarjejeniyar da aka kulla da su ba.
Kabiru Adamu, ya bayyana hakane a yayin tattaunawa da Explorer Hausa dangane da halin tabarbarewar tsaro a yankin arewa maso gabashin Najeriya, inda ya ce ba ya ga bayyana gaskiya kan abin da aka cimma, dole ne kuma gomnati ta samu amincewar ‘yan kasa game da wannan yarjejeniya.
A cikin wannan hira ta musamman, masanin ya bayyana dalilan da suka sa rashin tsaro ya tabarbare a faɗin ƙasar, yana nuna gibin da ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka ke amfani da shi tsawon shekaru tare da dora laifin ga yadda sararin samaniyar Najeriya ta kasance da gibi wajen samun kariya na tsaro.
Ya kuma bayar da dalilin da ya sa waɗannan ƙungiyoyin masu aikata laifuka ke aikata laifi ba tare da samun tsaiko ba, kuma ya yi gargaɗi game da wasu kalubale da ka iya afka wa ƙasar, ciki har da rashin daukan mataki na far wa ‘yan ta’adda inda a maimakon hakan jami’an tsaro ke jira har sai an kai hari kafin su mayar da martani.