Yan bindiga da ake zargin suna da alaƙa da ƙungiyar Lakurawa sun kai hari kan wani wurin binciken ’yan sanda a hanyar Bakinruwa zuwa Maje a ƙaramar hukumar Bagudo ta Jihar Kebbi, inda suka kashe jami’an ’yan sanda biyu da ke bakin aiki.
Harin ya faru ne a ranar Alhamis lokacin da maharan suka mamaye wurin binciken, suka buɗe wuta kan jami’an tsaro, kafin daga bisani su ƙone tantin da jami’an ke amfani da shi a wurin.
Mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya tabbatar da faruwar harin ga manema labarai, yana mai cewa jami’an ’yan sanda biyu sun rasa rayukansu yayin harin.
Rahotanni daga wasu mazauna yankin sun ce maharan sun zo da yawa inda suka mamaye wurin binciken, suka fi ƙarfin jami’an tsaron kafin su ƙona kayan aikin da ke wurin sannan suka tsere zuwa daji.
Harin ya ƙara tayar da fargaba a yankunan iyakar Kebbi, inda a baya ma aka ruwaito hare-haren da ake dangantawa da ƙungiyar Lakurawa a wasu ƙananan hukumomin jihar da ke kusa da iyaka.