Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

‘Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 11 a Kebbi

Sojoji Sojoji

Akalla jami’an tsaro 11 da suka hada da sojoji da ‘yan sanda sun rasa rayukansu a wani harin kwanton bauna da aka kai musu a garin Giron Masa, karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi.

Harin ya faru ne a daren Talata yayin da jami’an ke kan hanyarsu ta zuwa wata masana’anta domin gudanar da aikin tsaro, inda ‘yan bindiga suka tare su suka bude musu wuta.

Rahotanni sun nuna cewa, bayan musayar wuta tsakanin bangarorin biyu, ‘yan bindigar sun yi nasarar kashe jami’an tare da kona motocinsu guda biyu.

Bayan faruwar lamarin, gwamnan jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya ziyarci asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya domin duba wadanda suka jikkata tare da jajanta wa iyalan wadanda suka rasu.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use