Wasu ‘yan bindiga sun sace Limami da Ladanin wani masallaci a garin Dogon Ruwa da ke karamar hukumar Wase ta Jihar Filato.
Maharan sun kuma kashe mutum daya da sace wasu mutane shida.
Garin Dogon Ruwa na daya daga cikin garuruwan da ‘yan bindiga suka addaba wajen kai hare-hare a baya bayan nan.
Mazauna yankin sun tabbatar wa manema labarai cewa ‘yan bindigan sun yi awon gaba da mutanen ne yayin da suke tsaka da aikin gawayi wanda suke sayarwa.
Shugaban matasan karamar hukumar ta Wase, Shapi’i Sambo ya ce harin ya jefa tsoro da shakku cikin zukatan mazauna yankin.
Ya kara da cewa, bayan harin, al‘umma sun so su kai dauki amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba.
Sannan ya ce zuwa yanzu, an kai jami’an tsaro da zummar samar da zaman lafiya a yankin tare da kwantar wa al’ummar garin hankali.