Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Yan bindiga sun sace masu ibada shida a coci a Ondo

Wasu ’yan bindiga dauke da makamai sun sace masu bauta shida yayin gudanar da ibadar dare a jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya, lamarin da ke kara nuna kalubalen tsaro da ake fuskanta a wasu sassan kasar.

An kai harin ne da misalin karfe 12:50 na dare a wani reshen cocin Celestial Church of Christ da ke garin Uso, karamar hukumar Owo na jihar.

Shaidu sun ce maharan sun harba bindiga a sama domin tarwatsa masu ibadar, kafin su yi awon gaba da mutum shida zuwa wani wuri da ba a bayyana ba.

Rundunar ’yan sandan jihar Ondo ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an tura jami’ai zuwa wurin nan take bayan samun kiran gaggawa.

Kakakin rundunar, Jimoh Abayomi, ya ce jami’an tsaro sun ceto daya daga cikin wadanda aka sace tare da kama wani da ake zargi da hannu a harin, wanda yanzu haka yake bayar da bayanai domin taimakawa bincike.

Hukumomi sun bayyana cewa ana ci gaba da kokarin ceto sauran mutanen da aka sace tare da cafke sauran mambobin kungiyar.

A shekarun baya-bayan nan, sace-sacen mutane domin karbar kudin fansa ya zama ruwan dare wanda kuma ke barazana ga matafiya, dalibai da kuma cibiyoyin addini a sassan Najeriya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use