Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Yan bindiga sun sace mutum shida a Sokoto

Yan bindiga sun sace mutum shida a Sokoto Yan bindiga sun sace mutum shida a Sokoto
Yan bindiga sun sace mutum shida a Sokoto

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari wani ƙauye a jihar Sokoto inda suka sace mutum shida.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun shiga ƙauyen Gazau da ke karamar hukumar Isa da misalin ƙarfe 1:00 na dare, inda suka rika shiga gidaje suna kwashe mutane.

Da farko sun sace mutane 13, ciki har da mata 12 da namiji guda, amma daga bisani suka sake wasu bayan sun isa dajin Dan Adama, inda suka rarraba su bisa tsarin sakin wasu da riƙe wasu.

An tafi da mutum shida zuwa inda ba a sani ba, yayin da aka saki bakwai.

Haka kuma, maharan sun yi barazanar ci gaba da kai hare-hare a kullum idan mazauna yankin ba su nemi sulhu da su ba.H

ar zuwa yanzu, ba a samu martani daga jami’an gwamnati ko na ‘yan sanda ba kan wannan lamari.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use