‘Yan bindiga sun kutsa ƙauyen Kurmin-Uwa da ke ƙaramar hukumar Kagarko a jihar Kaduna, inda suka sace wata uwa da yara shida.
Harin ya zo ne ƙasa da sa’o’i 24 da ‘yan bindiga suka sace wasu mutane bakwai ‘yan gida ɗaya da wasu ƙarin mutum uku a Unguwar Sabon titin, Katari da ke jihar ta Kaduna.
Wani mazaunin garin Kagarko, mai suna Ibrahim Shehu, wanda ya tabbatar da satar uwa da yaran, ya shaida wa ƴan jarida cewa lamarin ya faru ne kusan ƙarfe 10:23 na daren Jumma’a.
Wani shugaban al’umma a yankin, wanda ya buƙaci a sakaye sunansa shima ya tabbatar da lamarin, inda ya ce ya sanar da jami’an tsaro bayan da ya samu labarin cewa ‘yan fashin daji sun kai hari ƙauyen, wanda, a cewarsa, yana da nisan kilomita 2 daga garin Kagarko.
“Bayan da na samu kiran neman agaji, na gaggauta sanar da jami’an tsaro, amma ban san sun je ko ba su je ba,” in ji shi.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Hassan Mansur, bai ɗaga waya ba kuma bai amsa saƙon manema labarai ba kan lamarin.