Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

‘Yan bindiga sun kashe mutum uku tare da garkuwa da wani fasto a Kaduna

'Yanbindiga sun sha far wa al'umma a jihar Kaduna 'Yanbindiga sun sha far wa al'umma a jihar Kaduna
'Yanbindiga sun sha far wa al'umma a jihar Kaduna

Wasu ‘yan bindiga sun halaka mutum uku tare da sace wani fasto Reverend Nathaniel Asuwaye a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya.

‘Yan bindigan sun kai harin ne a gidan faston da misalin karfe 3:20 na daren ranar Juma’ar da ta gabata a gidansa dake Karku a Karamar hukumar Kauru dake Jihar Kaduna.

Faston shi ne babban malamin cocin Katolika da ke ungwar Karku a karamar hukumar.

Sai dai a cikin wata sanarwa da cocin ya fitar ta bakin Reverend Jacob Shanet ya ce, bata gari ne suka kaddamar da harin don haddasa rigima a yankin.

Ya kara da cewa, wadanda aka kashe mazauna yankin ne, da suka hada da Jacob Dan’azumi da Maitala da Alhaji Kusari.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use