Daniel Bwala, mashawarcin shugaban kasa, ya bayyana cewa jam’iyyar ADC ba ta shirya tsaf don zaben 2027 ba, inda ya ce duk ‘yan jam’iyyar na da burin zama shugaban ƙasa ne kawai.
Bwala ya ce wannan rashin haɗin kai na nuna rashin tsari da niyya ta haɗin gwiwa a cikin jam’iyyar, wanda zai iya jefa ADC cikin matsaloli kafin babban zaben.
Ya ƙara da cewa zarge-zargen wasu jagororin ADC na cewa gwamnati na shirin murkushe jam’iyyarsu ba gaskiya ba ne, kuma abin ya samo asali ne daga rashin shirye-shiryen jam’iyyar.
A gefe guda, shugabannin ADC sun ce za su tsaya tsayin daka wajen fafatawa a zaben 2027 duk da matsalolin cikin gida, kuma INEC ba za ta hana su shiga zaben ba.