Mabiya darikar Kwankwasiyya sun yi tir da gaggauta amincewa da gyaran fuska da aka yiwa dokar zaɓe tare da sa hannun da shugaban ƙasan Najeriya Bola Tinubu ya yi.
A cewar ‘yan kwankwasiyya, wannan mataki na nuna barazanar ga jam’iyyun adawa da dimokuraɗiyya
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ƙungiyyar, Habibu Sale Mohammed ya fitar a Kano, mabiya darikar sun zargi jam’iyyar APC da amfani da rinjayen da take da shi a majalisar zartarwa don murƙushe ra’ayin jama’a.