Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske
Man United ta ci gaba da ba da mamaki a gasar Premier
‘Yan Najeriya na raina shugabanninsu, a ƙasashen waje kuma ana girmama su – Remi Tinubu
Hisbah ta kama masu aikata ‘baɗala’ 11 a Kebbi

‘Yan Najeriya na raina shugabanninsu, a ƙasashen waje kuma ana girmama su – Remi Tinubu

Uwargidan Shugaban Najeriya (Hoto: X Oluremi Tinubu)

Uwargidan Shugaban Najeriya Oluremi Tinubu ta fada cewa a yayin da ‘yan Najeriya ke raina jagororinsu, a can kasashen ketare kuma ana girmamasu.

Oluremi ta bayyana hakan ne a shafinta na Facebook a daren Juma’a bayan fitowarta daga wani taro a Amurka.

Har ila yau, ta ce mutane da dama na ganin shugabanni a matsayin abin ƙyama ko abin tsana a cikin Najeriya, duk da cewa a ƙasashen waje ana yabo da girmamasu saboda rawar da suke takawa da gudunmawar da suke bayarwa.

A cewarta, wannan rashin daraja da ake nuna wa shugabanni a gida ya samo asali ne daga “ƙiyayya da labaran ɓatanci” da wasu ‘yan siyasa ke yadawa a matsayin dabarar siyasa.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use