Rundunar ‘yan sanda a jihar Abia ta yi watsi da wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke nuna cewa an kama ‘yan Boko Haram 488 a jihar.
A cikin wata sanarwa da kakakin ‘yansandan DSP Maureen Chinaka ta fitar, ta ce tsohon bidiyo ne ake yawo da shi wanda ya kai fiye da shekaru 11, kuma bai nuna yanayın tsaro a jihar ba a yanzu.
Sun shawarci jama’a su ci gaba da ayyukansu cikin kwanciyar hankali, sannan su guji yada labaran karya, inda ta ce za a ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi a jihar.