Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama mata biyu da laifin safarar yara tare da ceto ‘yan mata uku a Yola.
Kakakin rundunar, SP Suleiman Nguroje ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a yau Laraba.
Nguroje ya ce sashin tattara bayanan sirrin hukumar ne sukayi aiki tukuru don kama yaran a tashar Adamawa Sunshine a ranar 17 ga Fabrairu, 2026.
Ya ce, “An ceto Naomi Linus (yar shekara 14), Agnes Thomas (yar shekara 16), da Patience Justine (yar shekara 15).”
Wadanda ake zargi sun hada da Hasiya Yuguda, mai shekaru 35, daga anguwar NEPA da ke karamar hukumar Yola ta Arewa, da kuma Ummulkhairi Abubakar, mai shekaru 40, daga Wuro-Hausa a Yola ta Kudu.