Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta tabbatar da mutuwar yara biyar sakamakon zargin gubar abinci a garin Takum, yayin da wasu takwas ke kwance a asibiti.
Kakakin rundunar, ASP Victor Mshelizah, ya ce yaran sun ci naman da ake zargin ya lalace a yayin wani karatun Ramadan.
Tuni aka fara bincike domin gano musabbabin lamarin.
Wani lauyan kare hakkin bil’adama a Jalingo, Barrista Bilyaminu Maihanci, ya bukaci gwamnati da hukumomin da abin ya shafa su gudanar da sahihin bincike domin tabbatar da adalci ga iyalan wadanda suka rasu.