Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da samun rahoton tsintar gawar wani mutum rataye a jikin bishiya a ƙasan Dutsen Bagale na ƙaramar hukumar Girei.
Tuni aka garzaya da gawar zuwa asibiti, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
Wani rahoton da ba na ‘yan sanda ba ya bayyana cewa marigayin mai suna Ahmed Mohammed mai shekara 46 shi ya kashe kansa ta hanyar rataya.
Ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin mutuwar mutumin a yanzu.
Rundunar ‘yansandan ta yi kira ga al’umma da duk wanda ke da wata muhimmiyar shaida da za ta taimaka wajen binciken da su fito su taimaka wa ‘yansanda.