Kamfanin rarraba wutar lantarki na Yola (YEDC) ya sanar da shirin katse wutar lantarki a jihohin Arewa maso Gabas domin gudanar da gyaran manyan kayayyakin wutar lantarki.
Rahotanni sun bayyana cewa za a rika samun katsewar ne a lokutan rana, daga ƙarfe 9 na safe zuwa 6 na yamma, na tsawon aƙalla kwanaki huɗu a kowane mako.
Kamfanin ya bayyana cewa an dauki wannan mataki ne don inganta tsarin lantarki da kuma ƙara ingancin samar da wuta a yankin bayan kammala aikin.
Sai dai an buƙaci al’umma da su yi haƙuri tare da ɗaukar matakan da suka dace lokacin katsewar, yayin da ake sa ran samun ingantacciyar wutar lantarki bayan kammala gyare-gyaren.