Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Za mu ci gaba da bai wa Tinubu cikakken goyon baya don cigaban kasa – Akpabio

Shugaban Majalisar Dattawa bayyana goyon bayan majalisa ga gwamnatin Tinubu Shugaban Majalisar Dattawa bayyana goyon bayan majalisa ga gwamnatin Tinubu
Akpabio ya jaddada cikakken goyon bayan majalisa ga gwamnatin shugaba Tinubu

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa majalisar tarayya tana bai wa gwamnatin shugaba Bola Tinubu cikakken goyon bayanta 100 bisa 100.

Akpabio ya ce haɗin kai tsakanin bangaren majalisa da kuma zartarwa na da matuƙar muhimmanci wajen samun ci gaba da inganta shugabanci a ƙasa.

Ya kuma yi watsi da masu sukar kusancin da ke tsakanin majalisa da gwamnati, inda ya ce irin wannan haɗin kai shi ne ke taimakawa ƙasashe su samu cigaba mai ɗorewa.

Shugaban majalisar ya tabbatar da cewa ‘yan majalisa za su ci gaba da bai wa gwamnatin Tinubu cikakken haɗin kai domin cimma manufofin ci gaban ƙasa.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use