Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

‘Za mu ci gaba da tattaunawa da Amurka’

Trump and Ayatollah Trump and Ayatollah
Shugaban Amurka Donald Trump da jagoran addini na Iran Ayatollah Khamenei

Manyan jami’an Amurka da na Iran sun ce za su ci gaba da tattaunawa bayan ganawar da suka yi a Oman kan batutuwan da suka haifar da fargabar ɓarkewar rikici tsakanin ƙasashen.

Ministan harkokin waje na ƙasar Iran, Abbas Araghchi ya ce tattaunawar da aka shiga tsakani ta kasance “mafari mai kyau”, kuma an mayar da hankali kan batun nukiliya ne kaɗai.

Ya ƙara da cewa a yanzu masu tattaunawa za su koma manyan biranen ƙasashensu domin tuntuɓar gwamnatocinsu.

Gabanin tattaunawar, jami’an Amurka sun ce suna son tattaunawa kan makamai masu linzami na Iran da kuma zargin da take yi ma ta na goyon bayan ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai a yankin, wanda ya nuna giɓin da ke tsakanin matsayin ƙasashen.

Gwamnatin Amurka dai ba ta ce komai kan batutuwan da aka tattauna ba kawo yanzu.

Tattaunawar ta kai tsaye da aka yi a birnin Muscat ta zo ne a daidai lokacin da ake ƙara jibge sojojin Amurka a yankin Gabas ta tsakiya domin mayar da martani ga mumunar murƙushe masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnatin Iran a watan da ya gabata.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use