Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta yi barazanar rufe mashigar Hormuz gaba ɗaya idan aka kai hari kan cibiyoyin makamashi da wutar lantarkin ƙasar.
IRGC ta ce idan ta rufe, ba za a bude ba har sai an sake gina wuraren makamashin da aka kai wa hari.
Cikin wata sanarwar da ta fitar, rundunar ta kuma ƙara da cewa za ta kai hare-hare tashoshin wutar lantarkin Isra’ila, cibiyoyin makamashi da cibiyoyin sadarwa, sannan kuma za ta lalata kamfanonin da Amurka ke da hannun jari a ciki a yankin gaba daya.
Ta kara da cewa, tashoshin makamashi a ƙasashen da ke da sansanonin sojin Amurka a yankin za su fuskanci hare-hare.
IRGC ta yi wannan barazanar ce bayan Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi iƙirarin yiwuwar kai hari kan cibiyoyin makamashi da wutar lantarki na Iran idan ba a bude mashigar Hormuz ba.