Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Za mu tabbatar da Tinubu ya samu nasara a zaben 2027 – Gwamnan Kebbi

Za mu tabbatar da Tinubu ya samu nasara a zaben 2027 - Gwamnan Kebbi Za mu tabbatar da Tinubu ya samu nasara a zaben 2027 - Gwamnan Kebbi
Gwamnan Jihar Kebbi, Dr Nasir Idris Kauran Gwandu

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana cewa jam’iyyar APC za ta tabbatar da cewa shugaban Bola Tinubu ya samu nasara a zaɓen shekarar 2027.

Gwamnan ya yi wannan furuci ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a Birnin Kebbi, inda ya ce sun tattauna muhimman batutuwan da suka shafi jam’iyyar tare da cimma matsaya.

Ya jaddada cewa jam’iyyar APC ta samu karɓuwa sosai a jihar, yana mai cewa al’ummar Kebbi na goyon bayan jam’iyyar kuma za su sake ba ta nasara a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya a 2027.

Taron ya samu halartar manyan jiga-jigan siyasa ciki har da ministan kasafin kuɗi, Atiku Bagudu, da sauran manyan shugabannin APC a jihar.

Gwamnan ya nuna kwarin gwiwar cewa APC za ta ci gaba da riƙe madafun iko a jihar Kebbi da ma ƙasa baki ɗaya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use