Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Za mu yi wa Walida adalci tare da kulawa da ita- Namadi

Umar Namadi ya karɓi yarinyar da aka sace, ya jaddada aniyar Gwamnati wajen kawo karshen shari’ar a kotu

Gwamnatin Jihar Jigawa ta karɓi ragamar kulawar Walida Abdulhadi Ibrahim, wata matashiya ‘yar asalin Jihar da ake zargin an sace ta, bayan da hukumar DSS suka miƙa ta a birnin Abuja.

Gwamnan ya bayyana cewa duk wasu batutuwa da suka shafi ɓacewarta da kuma zargin cin zarafi za a warware su ne ta hanyar kotu, inda ya tabbatar da cewa za a yi adalci ga kowa.

Rahotanni sun nuna cewa Walida ta ɓace ne tun shekarar 2023 daga Ƙaramar Hukumar Hadejia.

Lamarin ya sake fitowa fili ne a watan Disambar 2025, lokacin da mahaifinta ya samu labarin cewa tana Abuja.

Bayan shigar da ƙorafe-ƙorafe na shari’a da kuma umarnin kotu na a sake ta, DSS ta bayyana cewa tana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, lamarin da ya haifar da shari’a dangane da wanda ke da haƙƙin riƙonta.

Gwamna Namadi ya sha alwashin cewa Gwamnatin Jihar Jigawa za ta tabbatar da tsaron Walida, kare lafiyarta, da kuma ba ta cikakken tallafin farfaɗo da lafiyar kwakwalwa, bayan abin da ya bayyana a matsayin mummunan yanayi mai tayar da hankali da ta fuskanta.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use