Daruruwan matasa ƙarƙashin ƙungiyar Coalition for Goodluck Jonathan sun yi tattaki zuwa gidan Goodluck Jonathan a Abuja, inda suka buƙace shi da ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
An gudanar da tattakin ne a yankin Maitama na babban birnin tarayya FCT, inda masu zanga-zangar suka rika rera taken siyasa tare da ɗauke da allunan kira ga tsohon shugaban ya dawo fagen siyasa.
Shugaban ƙungiyar, Tom Ohikere, ya bayyana cewa sun yi dogon nazari a faɗin ƙasa, inda suka gano cewa jama’a da dama na son Jonathan ya dawo domin ceto ƙasar.
Ya ƙara da cewa suna ganin Jonathan na da ƙwarewa da kwarewar shugabanci da za su taimaka wajen magance matsalolin siyasa da tattalin arziƙin da Najeriya ke fuskanta.
Sai dai duk da jiran sa’o’i da suka yi, ba su samu ganawa da shi ba, domin an ruwaito cewa ba ya gida a lokacin.