Wasu da ake kyautata zaton ƴanbindiga sun kashe mutum 30 tare da sace wasu da dama a wani hari da suka kai ƙauyen Dutsin Dan Ajiya a karamar hukumar Anka na jihar Zamfara.
Hukumomi sun ce cikin waɗanda aka sace har da mata da ƙananan yara.
Maharan sun kutsa ƙauyen ne kan babura ranar Alhamis da dare zuwa safiyar Juma’a, inda suka toshe hanyar shiga garin tare da harbi kan mai uwa da wabi.
“Bayan toshe hanyar shiga garin, ƴanbindigar sun yi ta harbi inda jama’a suka yi ta gudu don tsira da ransu. Bayan harin ne muka gano cewa an kashe mutum 30, wasu sun jikkata sannan an tafi da wasu da dama babu wanda ya san inda suke,” in ji wani mazaunin garin.
Zamfara dai na ɗaya daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da matsalar ƴanbindiga ta addaba inda suke kashe mutane ba gaira ba dalili tare da sace dabbobi da lalata amfanin gona har ma da saka wa mutane haraji.