Wasu da ake zargin ƴanbindiga sun hallaka mutum shida tare da ƙona ofishin ƴansanda a karamar hukumar Borgu na jihar Neja.
Hukumomin ƴansanda a jihar sun ce lamarin ya faru ne da asubahin ranar Asabar lokacin da ƴanbindigar suka kutsa kauyen Tungan-Makeri inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi.
Mai magana da yawun ƴansanda a jihar, Wasiu Abiodun, ya ce an ƙona gidaje da dama tare da yin da garkuwa da mutane yayin harin.
Rahotanni sun bayyana cewa an fara kai hari ƙauyen na Tungan-Makeri ne tun ranar Juma’a, inda mahara sama da 200 suka yi dirar miƙiya a ƙauyen suna ta harbi da kuma ƙona gidaje.
Mazauna yankin sun yi iƙirarin cewa ƴanbindigar sun shafe sa’o’i suna buɗe wuta, lamarin da ya janyo mutuwar mutum shida tare da ɗaiɗaita wasu da dama.