Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Tinubu ya sabunta nadin Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Buba Marwa tsohon janar ne na sojan Najeriya Hoto: Facebook

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sabunta nadin Mohammed Buba Marwa a matsayin Shugaban Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) na tsawon shekara biyar.

Hakan na nuna cewa wa’adinsa zai kai har zuwa shekarar 2031. Marwa, ɗan asalin Jihar Adamawa ne ya fara shugabancin NDLEA a watan Janairun 2021, lokacin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Kafin wannan mukamin, ya shugabanci Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Kawar da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi daga 2018 zuwa Disamban 2020.

An sanar da sabunta nadin nasa ne a cikin wata sanarwa da Mai bai wa shugaban kasa shawara kan yada labarai Bayo Onanuga, ya fitar a ranar 14 ga Nuwamba, 2025.

Tinubu ya bayyana cewa sabunta nadin Marwa na nuna amincewa da irin nasarorin da ya samu wajen yaƙar ta’addancin fataucin miyagun ƙwayoyi a ƙasar.

Marwa na da digiri na biyu har guda biyu, na farko a Jami’ar Pittsburgh ta Pennsylvania a Amurka a shekarun 1983–85 da kuma ta Harvard a shekarun 1985–86 duk a Amurka.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use