Tun bayan sa-in-sa da ya auku a yammacin Talata, 11 ga Nuwamban 2025, tsakanin Ministan Abuja, Nyesom Wike, da wasu jami’an sojin Najeriya waɗanda suka hana shi shiga wani fili mai cece-kuce, lamarin ya zama abin tattaunawa a faɗin ƙasar.
Rahotanni da ra’ayoyi daban-daban sun rika yawo, amma abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne ko wane ne matashin hafsan sojin da ya tsaya a gaban ministan ba tare da nuna tsoro ba.
Wanda ya jagoranci tawagar sojojin shi ne Laftanar AM Yerima, a madadin tsohon Kwamandan Rundunar Sojan Ruwa, Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo mai ritaya, shi ne kuma mai filin da ake rikici a kai.
Ganin yadda Yerima ya tsaya ba tare da karkarwa ba duk da kakkausan kalamai da barazanar Wike ya sa mutane da dama mamaki, hatta wasu suna ganin jarunta ce ta musamman.
Wane neLaftanar Ahmed Mohammed Yerima?
An haife shi a Kaduna, ya tashi a can da kuma a Fatakwal, duk da cewa asalinsa dan garin Fune ne a Jihar Yobe.
Ya fara karatun aikin jarida a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) a 2011, inda abokan karatunsa suka ba shi laƙabin “MD” saboda halayensa na mutum mai nutsuwa, iya mu’amala da rashin tsoro.
Sai dai bayan shekara guda a ABU, ya bar jami’ar bayan samun gurbin shiga Makarantar Horar da Sojoji ta NDA a Kaduna a 2012. Daga nan ya kammala koyarwarsa ya zama Laftanar a Rundunar Sojan Ruwa a 2017.
A 2018, Yerima ya yi wani atisayen yaƙi da ta’addanci na ƙasa da ƙasa mai taken “Exercise Flintlock” a Agadez ta Jamhuriyar Nijar.
Duk da wasu rahotanni da suka danganta shi da tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Soji, Birgediya Janar Mohammed Yerima, bincike ya gano cewa mahaifinsa ba soja ba ne, sai dai hamshaƙin ɗan kasuwa ne da ke gudanar da harkokinsa a kudu maso kudu.
Wani abokin Yerima ya tabbatar da hakan, inda ya ce “Mahaifinsa mashahurin ɗan kasuwa ne. Ya mayar da iyalinsa daga Kaduna zuwa kudancin Najeriya, nan ne suka girma ciki har da Laftanar Yerima.”