Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

DSS ta kama dillalin makamai a Filaton Najeriya

DSS ta ce ta yi amfani da bayanan sirri wajen gano mai laifin (Hoto: DSS)

Rundunar tsaron farin kaya ta DSS ta kama wani dillalin makamai da ake zargi da safarar makamai ga ’yan bindiga a Jihar Filato dake Najeriya bayan wani samame da ta gudanar.

DSS ta kai samamen ne sakamakon sahihan bayanan sirri, a cewar sanarwar da hukumar ta fitar ranar Lahadi.

Rundunar ta ce an cafke wanda ake zargin, Musa Abubakar, ne a ranar Laraba, bayan bin sahun bayanan sirri da suka nuna cewa yana safarar makamai a unguwar Mista Ali da ke ƙaramar hukumar Bassa a Jihar Filato.

Sanarwar ta bayyana cewa Abubakar ya amsa laifin safarar manyan bindigogi da harsasai zuwa hannun ƙungiyoyin ’yan bindiga a Filato da wasu jihohin arewa.

DSS ta ƙara da cewa samamen ya yi nasara ne sakamakon wani bincike mai zurfi da ya kai ga gano hanyoyin safarar makaman da ake amfani da su wajen ta da tarzoma a yankin.

Hukumar ta ce ana ci gaba da bincike domin gano waɗanda ake zargin suna aiki tare da shi.

A daya banaren kuma, a ƙarshen makon da ya gabata, DSS ta sanar da sake kama Abdulazeez Obadaki, wanda aka fi sani da Bomboy, wanda ya tsere daga gidan gyaran hali na Kuje bayan harin da aka kai a shekarar 2022.

Ana zargin Bomboy da hannu a harin da aka kai cocin Owo na Jihar Ondo ashekarar 2022.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use