Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi kakkausar suka kan harin sama da aka kai kasuwar Jilli wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 50, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin takaici da kuma gazawa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Atiku ya nuna damuwarsa kan yadda ake kai wa fararen hula hare-hare da aka tsara kai wa ‘yan ta’adda, yana tambayar har yaushe ‘yan Najeriya za su ci gaba da fuskantar barazana daga bangarori daban-daban, ciki har da wadanda suka kamata su kare su?
Atiku ya jaddada cewa dole ne a sake nazari kan yadda ake tafiyar da harkokin tsaro a Najeriya, tare da ɗaukar alhakin abin da ya faru da kuma ɗaukar matakan gaggawa domin hana aukuwar irin wannan lamari a nan gaba.
Wazirin na Adamawa, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da al’ummomin da abin ya shafa, yana mai kira ga gwamnati da ta sauke nauyin da ke kanta na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa in da ya ce wannan shi ne ginshiƙin aikin tsaron ƙasa.