Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NiMet, ta yi gargadin cewa za a samu hadari da ruwan sama da kuma iska mai karfi a sassa daban-daban na Najeriya a ranar Litinin.
A cewar hasashen da hukumar ta fitar, yankunan Arewa za su fara da yanayi mai zafi da hasken rana da safe, amma daga baya ana sa ran samun hadari musamman a jihohin Adamawa da Taraba.
Hukumar ta kuma bayyana cewa yankunan tsakiyar ƙasar za su fuskanci gajimare da ɗan hasken rana da safe, kafin a samu hadari a wurare da dama ciki har da Abuja da Kogi da Kwara da kuma Filato.
A yankunan Kudancin ƙasar kuwa, ana sa ran samun gajimare tare da matsakaicin ruwan sama, wanda zai ƙaru da yamma, tare da yiwuwar samun iska mai ƙarfi da walƙiya.
Har ila ya, NiMet ta shawarci al’umma su ɗauki matakan kariya, ciki har da kula da abubuwan da iska za ta iya lalatawa da guje wa tuƙi cikin ruwan sama mai ƙarfi da kuma neman mafaka yayin walƙiya domin kauce wa haɗari.