Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Jigawa: Wani makusancin Badaru ya fice daga APC zuwa ADC

Jigawa: Wani makusancin Badaru ya fice daga APC zuwa ADC Jigawa: Wani makusancin Badaru ya fice daga APC zuwa ADC
Wani tsohon shugaban karamar hukuma a Jihar Jigawa, Shehu Sule Udi, ya fice daga jam’iyyar APC tare da komawa ADC, lamarin da ke ƙara girgiza siyasar jihar

Wani tsohon shugaban karamar hukuma a Jihar Jigawa, Shehu Sule Udi, ya fice daga jam’iyyar APC tare da komawa ADC, lamarin da ke ƙara girgiza siyasar jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa Udi ya dauki wannan mataki ne bayan tuntubar magoya bayansa da kuma nazari kan halin da jam’iyyar ke ciki a matakai daban-daban.

A cikin wasikar da ya rubuta, ya ce ya yanke shawarar ne saboda abin da ya kira sauyin akida da kuma tafiyar da jam’iyyar da ba ta dace da manufofinsa ba, yana mai cewa hakan ya sa ya kasa ci gaba da zama a APC.

Sauya sheƙar tasa zuwa ADC na daga cikin jerin sauye-sauyen siyasa da ke faruwa a Jigawa, inda wasu manyan ‘yan siyasa ke barin APC domin neman sabuwar mafita a wasu jam’iyyu.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use